BANGAREN FIQIHU.

Amsa- Tsarki: Shine ɗauke kari, da kuma kawar da dauɗa.
Tsarkin dauɗa:
Shine muslmi ya kawar da dukkan abinda ya afku na najasa akan jikinsa, ko akan tufafinsa, ko akan bigire da wurin da zai yi sallah acikinsa.
Tsarkin kari:
Shine wanda yake kasancewa a alwala ko wanka, da ruwa mai tsarkakewa, ko kuma taimama ga wanda ya rasa ruwa, ko kuma amfani da ruwan ya wuyata akansa.

Amsa- Ta hanyar wankeshi da ruwa har sai ya tsarkaka.
- Amma abinda kare yayi lallagi dashi, sai a wankeshi sau bakwai, na farkon da ƙasa.

Amsa- Annabi - tsira da aminci su tabbata agareshi - yace: "Idan bawa musulmi yayi alwala", ko kuma "Mumini", "sai ya wanke fuskarsa, to kowane kuskure zai fita daga fuskarsa da yayi duba zuwa gareshi da idanuwansa tare da ruwan", ko kuma "Tare da ƙarshen ɗigon ruwan", "Idan ya wanke hannayensa, kowane kuskure zai fita daga hannayensa waɗanda hannayensa suka damƙa dasu tare da ruwan" ko "Tare da ƙarshen ɗigon ruwan", "Idan ya wanke kafafuwansa kowane kuskuren da ƙafafuwansa suka tafi garesu zasu fita tare da ruwa ko tare da ƙarshen ɗigon ruwan" "Har sai ya fita tsarkakakke daga zunubai". Muslim ne ya rawaitoshi.

Amsa: Ka wanke tafuka sau uku.
Sai kayi kuskurar baki ka shaƙa ruwa, ka kuma face sau uku.
Kuskurar baki:
Shine sanya ruwa a baki, da kuma karkaɗa shi, da zubar dashi.
Shaƙa ruwa:
Shine: Jan ruwa ne ta iska zuwa cikin hanci da hannun damansa.
Facewa:
Shine fitar da ruwa daga hanci bayan shaƙawa, da hannun hagunsa.
Sannan wanke fuska sau uku.
Sannan wanke hannuwa biyu zuwa gwiwar hannu sau uku.
Sannan shafar kai, zaka fuskanto da hannayenka sannan kayi baya, sai ka shafi kunnuwa biyu.
Sannan ka wanke ƙafafuwanka biyu zuwa idan sawu sau uku.
Wannan shine mafi cika, haƙiƙa wannan ya tabbata daga Annabi - tsira da amincin Alla su tabbata agareshi - acikn hadisai acikin Bukhari da Muslim, waɗanda Usman da Abdullahi ɗan Zaid da wasunsu suka ruwaitosu. Kuma haƙiƙa ya tabbata a Bukhari da waninsa: "Lallai cewa shi yayi alwala sau ɗai-ɗai, kuma cewa shi yayi alwala sau biyu-biyu", ma'ana: Lallai cewa shi yana wanke kowacce gaɓa daga gaɓɓan alwala sau ɗai-ɗai, ko sau biyu-biyu.

Amsa- Sune waɗanda alwalar musulmi bata inganta idan yabar ɗaya daga cikinsu.
1. Wanke fuska, daga gareshi akwai kuskurar baki da shaƙa ruwa.
2. Wanke hannuwa biyu zuwa gwiwar hannaye biyu.
3. Shafar kai, daga gareshi akwai kunnuwa biyu.
4. Wanke ƙafafuwa biyu zuwa idon sawu biyu.
5. Jerantawa tsakanin gaɓɓai, ta yadda zai wanke fuska, sannan hannuwa biyu, sannan shafar kai, sannan wanke ƙafafuwa biyu.
6.Bibiya: Shine yin alwala a lokaci guda abin sadarwa, ba tare da rabawa ga lokacinba, har sai gaɓɓai sun bushe daga ruwa.
- Kamar yayi rabin alwalar, sai yacike ragowar awani lokacin daban, to alwalarsa bata ingantaba.

Amsa- Sunnonin alwala: Sune waɗanda da zai aikatasu to yana da ƙari na lada da sakamako, da zai barsu, to babu laifi akansa, kuma alwalarsa ingantacciyace.
1. Ambaton Allah: Bismillah.
2. Yin asuwaki.
3. Wanke tafukan hannu biyu.
4. Tsettsefe yatsu.
5. Wankewa na biyu da na uku ga gaɓɓai.
6. Farawa da dama.
7. Yin zikiri bayan alwala: "Ina shida cewa babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaɗai yake, bashi da abokin tarayya, kuma ina shaida cewa Annabi Muhammad bawansa ne kuma Manzonsane".
8. Yin sallah raka'a biyu bayanta.

Amsa- Abinda ya fita ta mafita guda biyu; gaban mutum da dubura, na fitsari da bayan gida da tusa.
Bacci, ko hauka, ko kuma suma.
Cin naman raƙumi.
Shafar gaba ko dubura da hannu ba tare da shamaki ba.

Amsa- Taimama: Itace amfani da turɓaya ko waninta daga bigiren ƙasa, yayin rasa ruwa, ko kuma wuyatar yin amfani dashi.

Amsa- Bugun kasa bugu ɗaya da cikin tafikan hannaye biyu, da shafar fuska, da bayan tafukan hannaye biyu sau ɗaya.

Amsa- Dukkan masu ɓata alwala.
Idan aka sami ruwa.

Amsa- Huffina biyu: Sune abinda ake sakawa a ƙafa na fata.
Safuna biyu:
Sune abinda ake sakawa a ƙafa waɗanda bana fata ba.
An halatta yin shafa akansu maimakon wanke ƙafafuwa biyu.

Amsa- Sauƙaƙawa da rangwami ga bayi, musamman acikin lokutan sanyi da ɗari da halin tafiya, ta yadda cire abinda ke cikin ƙafafuwa yake wahala.

Amsa- 1. Ya sanya huffi biyun akan tsarki, wato bayan alwala.
2. Huffin ya zama mai tsarki, shafa akan najasa bata halatta.
3. Huffin ya kasance mai rufewa ga wuri abin wajabta wankeshi acikin alwala.
4. Shafar takasance acikin mudda abar iyakancewa, ga mazaunin gida ba matafiyiba: Yini ɗaya da dare, matafiyi kuma: Kwana uku da dararensu.

Amsa- Siffar shafar itace: Ya sanya yatsun hannyensa biyu masu danshi da ruwa akan yatsun ƙafafuwansa biyu, sannan sai ya tafi dasu zuwa ƙwaurinsa, yana shafar ƙafar dama da hannun dama, ƙafar hagu da hannun hagu, zai kuma ware yatsunsa idan yayi shafar, kada ya maimaita.

Amsa- 1. Karewar kwanakin shafar, shafa akan huffi baya halatta bayan ƙarewar muddar shafar abar iyakancewa a shari'ah, yini da dare, ga mazaunin gari, da kwanaki uku da dararensu ga matafiyi.
2. Cire huffin biyu, idan mutum ya cire huffin biyu ko ɗayansu bayan shafarsa, to shafar akansu ta ɓaci.

Amsa- Sallah: Itace bautawa Allah da wasu maganganu da kuma wasu ayyuka keɓantattu, abar buɗewa da kabbara, abar rufewa sallama.

Amsa- Sallah wajibice akan kowanne musulmi.
Allah - maɗaukakin sark - yace: {Lallai Sallah ta kasance akan muminai farillace mai ƙayyadajjen lokaci 103}. [Surat Al-Nisa'i: 103].

Amsa: Barin sallah kafircine, Annabi - tsira da aminci su tabbata agareshi - yace:
"Alƙawari a tsakaninmu dasu shine sallah, wanda ya barta to ya kafirta".
Ahmad da Timizi ne da wasunsu suka ruwaitoshi.

Amsa- Salloli biyar ne a yini da dare, Sallar Asubah: Raka'oi biyu ce, da sallar Azahar: Raka'oi huɗu ce, da sallar La'asar: Raka'oi huɗu ce, da sallar Magariba: Raka'oi uku ce, da sallar Isha'i: Raka'oi huɗu ce.

Amsa: 1. Musulunci, bata inganta daga kafiri.
2.Hankali,bata inganta daga mahaukaci.
3. Wayo, bata inganta daga ƙaramin yaron da bashi da wayo.
4. Niyyah.
5. Shigar lokaci.
6. Tsarki acikin ɗauke hadasi.
7. Tsarkaka daga najasa.
8. Suturce al'aura.
9.Fuskantar Al-ƙiblah.

Amsa; Su rukunai goma sha huɗu ne, kamar yanda yake zuwa:
Na farkonsu: Tsayuwa acikin farilla ga mai iko.
Kabbarar Harama, itace: "Allahu Akbar".
Karatun Fatiha.
Ruku'u, sai ya miƙar da gadon bayansa adaidaice, ya kuma sanya kansa daidai da dashi.
Dagowa daga gareshi.
Daidaituwa alhali yana a tsaye.
Sujjada, da kuma tabbatar da goshinsa, da hancinsa, da tafukan hannayensa biyu, da gwiwowinsa biyu, da yatsun gefan diga-digansa daga awurin sujjadarsa.
Dagowa daga sujjada.
Zama tsakanin sujjada biyu.
Sunna:
Shine ya zauna yan mai shinfiɗa akan kafarsa ta hagu, yana kuma kafe kafarsa ta dama, yana mai fuskantar da ita zuwa Al-ƙiblah.
Nutsuwa, itace natsuwa akowane rukuni na aiki.
Tahiyar ƙarshe.
Zama domin shi.
Sallama biyu, shine yace sau biyu: "Assalamu alaikum wa rahmatullah".
Jeranta rukunai - kamar yadda muka ambata -, da zaiyi sujjada a misali kafin ruku'insa da gangan to ta ɓaci, idan kuma da rafkannuwane, to dawowa ya lazimceshi dan yayi ruku'u, sannan yayi sujjada.

Amsa- Wajiban sallah, su takwas ne, kamar yanda ke tafe:
I. Kabarbari, banda kabbarar Harama.
2. Faɗin: "Sami'Allahu Liman Hamidahu" ga liman damai sallah shi kaɗai.
3. Faɗin: "Rabbana walakal hamdu".
4. Faɗin: "Subhana Rabbiyal Azim", sau ɗaya acikin ruku'i.
5. Faɗin: "Subhana Rabbiyal A'alah", sau ɗaya acikin sujjada.
6.Faɗin: "Rabbighirli", tsakanin sujjada biyu.
7. Tahiyar farko.
8. Zama domin Tahiyar farko.

Amsa- Goma shaɗaya ne, kamar yanda yake tafe:
1.Faɗinsa bayan kabbarar Harama: "Subhanakallahumma, wabi hamdika, watabarakasmuka, wa ta'ala jadduka, wa la ilaha ghairuka". Ana ambatanta: Addu'ar buɗe sallah.
2. Neman tsari.
3. Yin Bisimillah.
4. Faɗin: Amin.
5.Karatun surah bayan fatiha.
6. Bayyanar da karatu ga liman.
7.Faɗin: "Mil'us samawati, wamil'ul ardhi, wa mil'u ma shi'ita min shai'in ba'adu". Bayan kammala Tahamidi.
8. Abinda yaƙaru akan ɗaya na Tasbihin ruku'i, wato: Tasbihi na biyu da na uku da abinda ya ƙaru akan haka.
9. Abinda ya ƙaru akan ɗaya a tasbihin sujjada.
10. Abinda ya ƙaru akan ɗaya a faɗinsa: "Rabbig firli" Tsakanin sujjada biyu.
11.Yin salati a tahiyar ƙarshe ga iyalansa - tsiran da amici ya tabbata agaresu -, da albarka a gareshi da kuma su, da yin addu'a bayansa.
Na huɗu:
Sunnoni na ayyuka, ana ambatansu Al-Hai'at.
1. Daga hannu tare da kabbarar Harama.
2. Da yayin yin ruku'u.
3. Da kuma lokacin ɗagowa daga ruku'in.
4. Da sakko dasu bayan hakan.
5. Dora hannun dama akan na hagu.
6. Dubansa zuwa bigiren sujjadarsa.
7. Warawarsa tsakanin diga-digansa biyu alhali yana tsaye.
8. Damƙar gwiwowinsa da hannayensa, yana mai wara yatsun hannaye a ruku'insa, da kuma miƙar da gadon bayansa acikinsa, da sanya kansa daura dashi.
9. Tabbatar da gaɓuɓuwan sujjada a ƙasa, da kuma damƙar ƙasar ga bigiren sujjada.
10. Buɗa damatsansa ga gefunansa biyu, da kuma raba cikinsa ga cinyoyinsa, da raba cinyoyinsa ga ƙwaurikansa, da rabawarsa tsakanin gwiwowinsa, da tsayar da diga-digansa, da sanya cikin yatsunsu akan ƙasa yana mai rabawa, da sanya hannuwansa daura da kafaɗunsa a shinfide, yatsun kuma a dunƙule.
11. zaman Iftirashi a zama tsakanin sudda biyu, da a zaman Tahiya na farko, da kuma zaman Tawarruk a zama na biyu.
12. Dora hannaye akan cinyoyi suna a shinfiɗe, yatsun a dunƙule tsakanin sujjadu biyu, haka kuma a Tahiya, sai dai cewa shi anan zai damƙi daga ƙaramin ɗan yatsa na gefe dama da mai binsa, yakuma naɗe babban yatsa tare da na tsakiya, yana mai nuni da manuniyarsu yayin ambaton Allah.
13. Juyawarsa dama da hagu acikin sallamarsa.

Amsa-1. Barin wani rukuni ko sharaɗi daga sharuɗɗan sallah.
2. Yin magana da gangan.
3. Ci ko sha.
4. Motsi mai yawa a jere.
5. Barin wani wajibi ɗaya daga cikin wajibabbun sallah da gangan.

Amsa: Siffar yadda ake sallah.
1.Ya fuskanci Al-ƙibla da dukkanin jiknsa, batare da karkacewaba, ko kuma waiwaye.
2. Sannan yayi niyyar sallar da yake son ya sallaceta a zuciyarsa ba tare da furta niyyar ba.
3. Sannan yayi kabbarar Harama, sai yace: (Allahu Akbar), ya ɗaga hannayensa biyu zuwa daidai da kafaɗunsa biyu yayin kabbarar.
4. Sannan yaɗora tafin hannunsa na dama a bayan tafin hannunsa na hagu a saman ƙijinsa.
5. Sannan yayi addu'ar buɗe sallah, sai yace: "Ya Allah ka nesantar da tsakanina da kurakuraina kamar yadda ka nesanta tsakanin mahudar rana da mafaɗarta, ya Allah ka tsaftaceni daga kurakuraina kamar yadda ake tsaftace farin tufa daga datti, ya Allah ka wankeni daga kurakuraina da ruwa da ƙanƙara da kuma kumfa".
“Subhanakal Lahumma Wabi Hamdika, Tabarakas Muka, Wata’ala Jadduka, Wala’ilaha Gairaka”.
6.Sannan ya nemi tsari, sai yace: "Ina neman tsarin Allah daga Shaiɗan abin jefewa. 7. Sannan yayi Bisimillah, ya karanta Fatiha sai yace: {Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai 1. Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai 2. Mai Rahama Mai Jin Qai 3. Mamallakin Rãnar Sakamako 4. Kai kaɗai muke bautawa, kuma Ka kaɗai muke neman taimakonKa. Ka shiryar da mu hanya madaidaiciya 6. Hanyar waɗanda Kayiwa ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi akansuba, kuma ba ɓatattu ba 7}. [Fatiha: 1-7].
Sannan yace:
(Amin), yana nufin: Ya Allah ka amsa.
8.Sannan ya karanta abinda ya sawwaƙa na Al-ƙur'ani, sai ya tsawaita karatu a sallar Asuba.
9. Sannan yayi ruku'u: Wato ya sunkuyar da kansa, domin girmamawa ga Allah, ya kuma yi kabbara yayin ruku'insa, sai ya ɗaga hannayensa zuwa daura da kafaɗunsa. Sunnah: Itace ya miƙar da gadon bayansa, ya ɗora kansa daidai dashi, ya ɗora hannayensa akan gwiwowinsa biyu, yana mai wara yatsu.
10. Yana mai cewa acikin ruku'insa: "Tsarki ya tabbata ga Ubangijina Mai girma}. sau uku, idan kuma ya ƙara da: "Tsarki ya tabbatar maka ya Allah da godiyarka, ya Allah ka gafartamini" to yana da kyau.
11. Sannan ya ɗago kansa daga ruku yana mai cewa: "Allah yaji wanda ya gode masa", sai ya ɗaga hannayensa a wannan lokacin zuwa daura da kafaɗunsa biyu. Mamu kuwa ba zaice: "Allah yaji wanda ya gode masa", kawai a maimakonta sai yace: "Ya Ubangijinmu godiya ta tabbata gareka".
12. Sannan yace bayan ɗagowarsa: "Ya Ubangijimmu, godiya ta tabbata gareka cikin sammai da ƙasa, da kuma cikin abinda kaso na kowanne abu bayan haka".
13. Sannan yayi sujjadar farko, sai yace ayayin sujjadarsa: "Allahu Akbar", kuma zaiyi sujjadar ne akan gaɓɓai bakwai: Goshi, da hanci, da tafukan hannu biyu, da gwiwowi biyu, da gefunan yatsun ƙafafuwa biyu, sai nisantar da damutsansa daga gefunan jikinsa biyu, kada ya shinfiɗa zangalalin hannayensa biyu akan ƙasa, ya kuma fuskanci Al-ƙibla da kan yatsunsa.
14. Sai yace acikin ruku'insa: "Tsarki ya tabbata ga Ubangijina mafi ɗaukaka" sau uku, idan ya ƙara: "Tsarki ya tabbatar maka ya Allah Ubangijinmu, ya Allah ka gafarta mini" to yana da kyau.
15. Sannan ya ɗago kansa daga sujjada yana mai cewa: "Allah ne mafi girma".
16. Sannan ya zauna tsakanin sujjada biyu, akan diddigensa na hagu, sai ya kafa diddigensa na dama, sai ya ɗora hannunsa na dama akan gefan cinyarsa ta dama, daga inda yake biye da gwiwarsa, sai ya dunƙule ƙaramin yatsa da wanda yake bi masa, sai kuma ya ɗaga manuniya yana mai motsashi a yayin addu'arsa, yana sanya gefan babban yatsa haɗe da yatsan tsakiya kamar kewaye, sai ya ɗora hannunsa na hagu yatsun a shimfiɗe akan gefen cinyarsa ta hagu daga inda yake biye da gwiwa.
17. Sai yace acikin zamasa tsakanin sujjadu biyu: "Ya Ubangijina ka gafarta mini, ka ji ƙaina, ka shiryar dani, ka azurtani, ka datar dani, ka yi mini afuwa".
18. Sannan ya sake yin sujjada ta biyu kamar ta farko cikin abinda ake faɗa, kuma ake aikatawa, ya kuma yi kabbara yayin sujjadarsa.
19. Sannan ya miƙe daga sujjada ta biyun yana mai cewa: "Allah ne mafi girma" yana sallatar raka'a ta biyu kamar ta farko acikin abinda ake faɗa da abinda ake aikatawa, sai dai cewa shi ba zai sake addu'ar buɗe sallah acikinta ba.
20. Sannan ya zauna bayan ƙare raka'a ta biyu yana mai cewa: "Allah ne mafi girma", sai ya zauna kamar yadda ya zauna a tsakanin sujjada biyu daidai wadaida.
21. Sai ya karanta Tahiya a wannan zaman, sai yace: "Gaisuwa ta tabbata ga Allah da addu'oi da kyawawan abubuwa, aminci ya tabbata a gareka, ya kai wannan Annabi, da rahamar Allah da albarkarsa, aminci ya tabbata agaremu da salihan bayin Allah, ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaidawa cewa lallai Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa ne, Allah kayi tsira ga Muhammad da iyalan Muhammad, kamar yadda kayi salati ga Ibrahim da iyalan Ibrahim, lallai kai abin yabone mai girma, kayi albarka ga Muhammad da iyalan Muhammad, kamar yadda kayi albarka ga Ibrahim da iyalan Ibrahim, lallai cewa kai abin yabone kuma mai girma". Sannan sai ya roƙi Ubangijinsa da abinda yaso, na alhairan Duniya da lahira.
22. Sannan yayi sallama a damansa yana mai cewa: "Aminci ya tabbata agareku da rahamar Allah". Da kuma hagunsa kamar haka.
23. Idan sallar ta zama mai raka'a uku ce ko huɗu,ya tsaya inda ƙarshen Tahiyar farko take, shine: "Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaidawa lalle Annabi Muhammadu bawansane kuma Manzonsane".
24. Sannan sai ya yunƙura yana mai cewa: "Allah ne mafi girma", yana ɗaga hannayensa zuwa daidai kafaɗunsa a daidai wannan lokacin.
25. Sannan sai ya sallaci abinda yayi saura na sallarsa akan siffar raka'a ta biyu, sai dai cewa shi zai taƙaita ne akan karatun Fatiha kaɗai.
26. Sannan sai ya zauna zama na Tawarruƙ, yana kafa diddigen ƙafarsa tadama, yana kuma fitar da diddigen ƙafarsa ta hagu ta ƙarkashin ƙwaurinsa na dama, sai ya tabbatar da mazauninsa a ƙasa, sai kuma ya ɗora hannuwansa akan cinyoyinsa akan siffar ɗorasu aTahiyar farko.
27. A wannan zaman zai karanta Tahiya ne baki ɗayanta.
28. Sannan yayi sallama a damarsa yana cewa: "Assalamu alaikum warahmatullah". hakama a hagunsa.

Amsa: "Ina neman gafarar Allah" Sau uku.
"Ya Allah, kai ne aminci, kuma aminci daga gareka yake, ka girmama ya ma'abocin girma da ɗaukaka".
-"Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaɗai yake bashi da abokin tarayya, mulki nasane, kuma godiya tasace, shine mai iko akan komai. Ya Allah babu mai hanawa ga duk abinda ka bayar, kuma babu mai bayar da abinda ka hana, rabo baya amfanar da mai rabon gareka".
-"Babu abin bauta wa da gaskiya sai Allah, shi kaɗai yake bashi da abokin tarayya, mulki nasane kuma godiya tasace, kuma shi mai ikone akan komai, babu dabara, babu ƙarfi sai ga Allah, babu abin bauta wa da gaskiya sai Allah, ba ma bauta wa kowa sai shi, ni'ima tasace, falala tasace, kyakkyawan yabo nasane, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, muna masu tsarkake addini domin shi, ko da kafirai sun ƙi.
-"Tsarki ya tabbata ga Allah" sau talatin da uku.
-"Godiya ta tabbata ga Allah" sau talatin da uku.
-"Allah ne mafi girma" sau talatin da uku.
Sannan cikon ɗarin yace:
"Babu abin bauta wa da gaskiya sai Allah, shi kaɗai yake, bashi da abokin tarayya, mulki nasane kuma godiya tasace, kuma shi mai iko ne akan komai".
-Sai ya karanta Suratul Ikhalasi, da Falaƙi da Nasi sau uku, bayan sallar Asuba da Magariba, sau ɗaiɗai kuma bayan sauran sallolin.
- Sai ya karanta Ayatul Kursiyyi sau ɗaya.

Amsa: Raka'a biyu kafin Asuba.
Raka'a huɗu kafin Azahar.
Raka'a biyu bayan Azahar.
Raka'a biyu bayan Magariba.
Raka'a biyu bayan Isha.'i.
Falalarsu:
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - yace: "Wanda ya sallaci raka'a goma sha biyu a dare da rana domin neman lada, Allah zai gina masa gida a Aljanna". Muslim da Ahmad ne da wasunsu suka ruwaitoshi.

Amsa: Ranar Juma'a, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - yace: "Lalle yana daga cikin mafificin ranakunku ranar Juma'a, acikintane aka halicci Annabi Adam, kuma acikintane aka karɓi rayuwarsa, kuma acikintane za'a busa ƙaho, kuma acikintane za'a mutu, ku yawaita yin salati agareni acikinta, domin salatinku abin bijirowane agareni". Yace: Sukace Ya Ma'aikin Allah, to yaya za a bijiro da salatimmu agareka alhali haƙiƙa ka dandaƙe? - suna cewa ka dandaƙe - sai yace: "Lalle Allah - mai girma da ɗaukaka - ya haramta wa ƙasa jikin Annbawa". Abu Daud da waninsane suka ruwaitoshi.

Amsa: Farilace akan kowanne musulmi namiji baligi mai hankali mazauni.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan anyi kirã zuwã ga salla a rãnar Jumu'a, sai kutaho zuwa ga ambaton Allah, kuma ku bar ciniki. Wancan ɗinku ne mafi alhẽri agareku idan kun kasance kunã sani}. [Surat Al-Munafiƙun: 9].

Amsa: Adadin rakao'in sallar Juma'a raka'o'i biyu ne, liman yana bayyanar da karatunsu, huɗubobi biyu sanannu suna gabatarsu.

Amsa: Ba ya halatta ƙin zuwa sallar Juma'a, saidai idan akwai wani halataccen uzuri, yazo daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - faɗinsa: "Wanda ya bar Juma'a uku dan wulaƙantarwa, Allah zaiyi rufi akan zuciyarsa". Abu Daud ne da waninsa suka ruwaitoshi.

Amsa:
1. Wanka.
2. Shafa turare.
3. Sanya mafi kyan tufafi.
4. Zuwa masallaci da wuri.
5.Yawaita salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -.
6. Karatun Suratul Kahf.
7. Tafiya zuwa masallaci da ƙafa.
8. Kardadon lokacin amsa addu'a.

Daga Abdullahi ɗan Amr - Allah ya yarda dasu - lallai cewa Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - yace: "Sallar Jam'i tafi sallar mutum ɗaya da daraja ashirin da bakwai. Muslim ne ya ruwaitoshi.

Amsa: Shine halartar da zuciya da nutsuwar gaɓɓai.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Hakika mũminai sun rabauta}. {Waɗanda su suke yin khushu'i acikin sallarsu}. [Surat Al-Muminun: 1,2].

Amsa- Ita haƙƙi ce na wajibi a dukiya keɓantacciya ga wata jama'a keɓantacciyya a lokaci keɓantacce.
- Kuma ita rukuni ce daga cikin rukunan Musulunci, kuma sadaka ce ta wajibi da ake karɓa daga mawadaci a bada ita ga mabuƙaci.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Kuma suka bada Zakkah}. [Surat Al-Baƙarah: 43].

Amsa- Itace wacce ba zakkah ba, kamar: Yin sadaka ta fuskokin alheri kuma akowane lokaci.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Ku ciyar acikin tafarkin Allah}. [Surat Al-Baƙarah: 195].

Amsa- Shine yin bauta sabo da Allh ta hanyar kamewa daga barin abinda ke karya azumi, tun daga hudowar Alfiji har zuwa faɗuwar rana tare da niyya, shi kashi biyune:
Azumin wajibi: Kamar Azumin watan Ramadan, shi kuma rukuni ne daga cikin rukunan musulunci.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan waɗanda suke daga gabãninku, tsammãninku, zã ku yi taƙawa}. [Surat Al-Baƙarah: 183].
Da Azumin da bana wajibi ba:
Kamar Azumin ranar Litinin da Alhamis a kwanne sati, da Azumin kwanaki uku a kowanne wata, mafificin su kuma sune fararan kwanaki (13,14,15) na kowanne watan Musulunci.

Amsa- Daga Abu Huraira - Allah ya yarda dashi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - yace: "Wanda ya azumci Ramadan yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa abinda ya gabata daga zunubansa". An haɗu akansa (Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi).

Amsa- Daga Abu Sa'id Al-Khudri- Allah ya yarda dashi - yace: Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - yace: "Babu wani bawa da zaiyi Azumin wani yini ɗaya domin Allah, face sai Allah ya nesantar da fuskarsa daga wuta sanadiyyar wannan Azumin shekara saba'in". An haɗu akansa (Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi).
- Ma'ana "Kharif saba'in" wato; Shekara saba'in.

Amsa- 1- Ci da sha da gangan.
2. Kakalo amai da gangan.
3. Ridda daga musulunci.

Amsa-1- Gaggauta buɗa baki.
2. Sahur da kuma jinkirtashi.
3. Kari akan ayyukan alheri da kuma ibada.
4. Faɗar mai Azumi idan aka zageshi: Lallai ni ina Azumi.
5. Yin addu'a a lokcin buɗa baki.
6. Yin buɗa baki da ɗanyen dabino ko busasshe, idan kuma bai samu ba sai yayi da ruwa.

Amsa: Hajji: Shine yin bauta ga Allah - maɗaukain sarki - da nufin ɗakinsa mai alfarma domin gabatar da wasu ayyuka keɓantattu, a lokaci keɓantacce.
Allah Maɗaukakin sarki yace:
{Kuma akwai Hajjatar ɗaki domin Allah akan mutane ga wanda ya samu ikon zuwa gareshi wanda ya kafurce to lallai Allah mawadacine ga barin talikai}. [Surat Aal Imran: 97].

Amsa: 1. Harama (Niyya).
2. Tsayuwar Arafah.
3.Dawafin Ifadah.
4. Tafiya tsakanin Safa da Marwa.

Amsa- Daga Abu Huraira - Allah ya yarda dashi - yace: Naji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - yana cewa: "Wanda yayi Hajji, bai yi kwarkwasa ba, kuma bai yi fasikanci ba, zai dawo kamar ranar da mahaifiyarsa ta haifeshi". Bukhari da waninsa ne suka rawaito shi.
- "Kamar ranar da mahaifiyarsa ta haifeshi" Wato ba tare da wani zunubi ba.

Amsa: Umara ita ce bauta wa Allah da niyyar fuskantar ɗakinsa mai alfarma domin gabatar da ayyuka keɓantattu, a lokaci keɓantacce.

Amsa: 1. Harama (Niyya).
2. Dawafin a ɗakin Ka'abah.
3. Tafiya tsakanin Safa da Marwa.

Amsa: Shine bada ƙoƙari domin yaɗa Addinin musulunci da kuma kare shi, da ma abotansa, ko kuma yaƙar maƙiyi ga musulunci da ma abotansa.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Kuyi jihãdi da dũkiyõyinku da kuma rãyukanku a cikin hanyar Allah. Wancan ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance kunã sani}. [Surat Al-Tubah: 41].