BANGARAN TAUHIDI

Amsa - Ubangijina shine Allah wanda ya renenini, kuma ya reni dukkanin halitta da ni'imarsa.
Dalili:
Faɗinsa - madaukakin sarki-: (Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai 2). [Suratul Fatiha].

Amsa - Addini na shine Musulunci, shine: Miƙa wuya ga Allah da Tauhidi, da jawuwa gareshi da biyayya, da kuɓuta daga shirka da ma'abotanta.
Allah -maɗaukakin sarki - yace: {Lallai Addini a wajen Allah shine Musulunci}. [Suratul Aal Imran: 19].

Amsa: Shine Annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -.
Allah -maɗaukakin sarki - yace: {Muhammad Manzon Allah ne}. [Suratul Fathi: 29].

Amsa- Kalmar Tauhidi: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah" Ma'anarta: Babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah.
Allah -maɗaukakin sarki - yace: {Ka sani, cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah}. [Suratu Muhammad: 19].

Amsa: Allah yana sama, asaman Al'Arshi, a saman dukkanin halittu. Allah - maɗaukain sarki - yace: {Mai rahama, Ya daidaita a kan Al'Arshi}. [Suratu Daha: 5}. Kuma yace: {Shĩne marinjayi a kan bayinsa, kuma shine Mai hikima, Masani}. [Suratul An'am: 18].

Amsa- Ma'anarta: Lallai cewa Allah ya aiko shi ga dukkanin talikai mai bushara kuma mai gargadi.
Yana wajaba:

1. Yi masa biyayya a dukkanin abinda yayi umarni.
2. Gasgatashi acikin dukkanin abinda ya bada labari.
3. Rashin saɓa masa.
4 Ba'a bautawa Allah sai da abinda ya shar'anta, wannan shine koyi da Sunnah da kuma barin Bidi'a.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Dukkan wanda yabi Manzo to haƙiƙa yabi Allah} [Al-Nisa'i: 80], Kuma - tsarki ya tabbatar masa - yace: {Kuma ba ya furuci daga san zuciya, shi bai zamoba, sai wahayi ne da akeyi masa 4}. [Suratu Al-Najmi: 3-4]. Kuma Allah - mai girma da ɗaukaka - yace: {Haƙiƙa koyi kyakykyawa ya kasance gare ku daga Manzon Allah, ga wanda ya kasanee yanã ƙaunar Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya ambaci Allah da yawa 21}. [Suratu Al-Ahzab: 21].

Amsa- Ya halicce mu ne dan bauta masa shi kaɗai ba shi da abokin tarayya.
Badan wargiba ko wasa.
Allah -maɗaukakin sarki - yace: {Kuma ban halicci Aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta mini 56}. [Suratu Al-Zariyati: 56].

Amsa- Ita suna ne mai tattarowa ga dukkanin wani abin da Allah yake sonsa, kuma ya yarda dashi daga maganganu da ayyuka na ɓoye dana bayyane.
Na bayya ne:
Kamar ambaton Allah da harshe daga Tasbihi da godewa, Allah da yin Kabbara da sallah da Hajji.
Na ɓoye:
Kamar dogaro ga Allah, da tsoro, da ƙauna.

Amsa- Mafi girman wajibi akammu shine: Kaɗaita Allah - maɗaukakin sarki -.

Amsa- 1. Tuhidi na Rububiyyah: Shine imani da cewa Allah shine Mahalicci, Mai azurtawa, Mamallaki Mai juya al'amura, shi kaɗai yake, bashi da abokin tarayya.
2. Tuhidi na Uluhiyya: Shine kaɗaita Allah da bauta, baza'a bautawa wani ɗaya ba sai Allah - maɗaukakin sarki -.
3. Tauhidi na Sunaye da Siffofi: Shine yin imani da dukkanin sunaye da siffofi na Allah - maɗaukakin sarki - waɗanda sukazo acikin littafi da Sunna, batare da misaltawa, ko kamantawa ko korewa ba.
Dalilin Nau'ukan tauhidi guda uku:
Faɗin Allah - maɗaukakin sarki -: {Shine Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, to sai ka bauta masa, kuma kayi haƙuri ga bautarsa. Shin kã san wani takwara gareshi 65}. [Suratu Maryam: 65].

Amsa- Shirka da Allah - maɗaukikin sarki -.
Allah -maɗaukakin sarki - yace: {Lalle Allah baya gãfarta ayi shirki dashi, kuma yana gãfarta abin da yake bãyan wannan ga wanda yake so, kuma wanda yayi shirki da Allah, to, lalle ne ya ƙirƙiri zunubi mai girma 48}. [Suratu Al-Nisa'i: 48].

Amsa- Shirka: Itace juyar da kowane nau'i daga cikin nau'ikan ibada ga wanin Allah - maɗaukakin sarki -.
Nau'ukanta:

Babbar shirka, Misali: Kiran wanin Allah - maɗaukakin sarki -(kira na bauta) ko yin sujjada ga wanin Allah - tsarki ya tabbatar masa - ko kuma yanka ga wanin Allah - mai girma da ɗaukaka -.
Karamar Shirka, misali: Rantsuwa da wanin Allah - maɗaukakin sarki -,ko layu, shine abinda ake ratayawa daga abubuwa dan jawo wani amfani, ko tunkuɗe wata cuta, da sassauƙan riya, kamar ya kyautata sallarsa dan abinda yake gani daga kallon mutane zuwa gareshi.

Amsa- Babu wani wanda yasan gaibu sai Allah shi kaɗai.
Allah -maɗaukakin sarki - yace: {Kace bãbu wanda ya san gaibi a cikin sammai da ƙasa fãce Allah. Kuma bã su sansancẽwar a yaushe ne zã a tãyar da su 65}. [Suratu Al-Naml: 65].

Amsa- 1. Imani da Allah - maɗaukakin sarki -.
2. Da Mala'ikun sa.
3. Da Littatafan sa.
4. Da Manzannin sa.
5. Da ranar ƙarshe.
6 Da Kaddara alherinsa da kuma sharrinsa.
Dalili:
Shine Hadisin nan shahararre na Jibrilu, a wajen Muslim, Jibrilu yacewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -: "Kabani labari game da imani, yace: Kayi Imani da Allah, da Mala’ikunsa, da littattafansa, da Manzanninsa, da ranar Lahira, kuma kayi imani da ƙaddara alherinsa da sharrinsa".

Amsa: Imani da Allah.
Ka yi imani da cewa Allah shi ne wanda ya halicceka kuma ya azurtaka, shine kuma mamallakin halittu mai jujjuya lamuran halittu shi kaɗai.
Shine kuma abin bautawa, babu wani abin bauta wa da gaskiya sai shi.
Kuma shi ne mai cikakken girma, wanda yake dukkan godiya ta tabbata gareshi, kuma shi ke da sunaye kyawawa da kuma siffofi maɗaukaka, bashi da abokin tarayya, kuma wani abu baiyi kama dashi ba, tsarki ya tabbatar masa.
Imani da Mala'iku:

Sune ababen halittar da Allah ya halicce su daga harske,kuma domin bautarsa, da cikakken jawuwa ga umarninsa.
Daga cikinsu akwai Jibrilu - amincin Allah ya tabbata agareshi - wanda yake saukar da wahayi ga Annabawa.
Imani da Litattafai:

Sune littattafan da Allah ya saukar da su ga Manzanninsa.
- Kamar Al-ƙur'ani: Ga Annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -.
- Injila: Ga Annabi Isa - amincin Allah ya tabbata agareshi -.
- Attaura ga Annabi Musa - amincin Allah ya tabbata agareshi -.
- Zabura ga Annabi Dawud - amincin Allah ya tabbata agareshi -.
- Takardun Annabi Ibrahim da Annabi Musa; Ga Ibrahim da Musa.
Imani da Manzanni:

Sune waɗanda Allah ya aiko su zuwa ga bayinsa, domin su ilmantar dasu, kuma suyi musu bushara da alheri da Aljanna, su kuma yi musu gargaɗi da sharri da kuma wuta.
- Mafifitansu: Sune Ulul Azmi, sune:
Annabi Nuhu - aminci ya tabbata agareshi -.
Annabi Ibrahim - aminci ya tabbata agareshi -.
Annabi Musa - aminci ya tabbata agareshi -.
Annabi Isa - aminci ya tabbata agareshi -.
Annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -.
Imani da Ranar Lahira:

Shine abinda yake bayan mutuwa, a ƙabari, da ranar Al-ƙiyama, ranar tashi daga ƙabari, da hisabi, yadda 'yan Aljanna zasu tabbata acikin masaukansu, da 'yan wuta acikin masaukansu.
Imani da ƙaddara alherinsa da kuma sharrinsa:

Kaddara: Shine ƙudurcewa a zuciya cewa Allah yana sanin dukkan wani abu da yake kasancewa a kasantattu, kuma cewa shi ya rubuta wannan abin acikin Lauhul Mahfuz, kuma yaso samuwarsa da kuma halittarsa.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Lalle ne mu kowanne abu mun halicce shi da ƙaddara 49}, [Suratu Al-kamar: 49].
- Shi yana kan matakai huɗu:
Na ɗaya: Sanin Allah - maɗaukakin sarki - yana daga wannan saninsa wanda ya rigayi dukkan komai, kafin afkuwar abubuwa da bayan afkuwarsu.
Dalilinsu:
faɗin Allah - maɗaukakin sarki -: {Lalle Allah a wurinsane kawai sanin Al-ƙiyama, kuma yanã saukar da girgije, kuma yanã sanin abin da yake a cikin mahaiffannai, kuma wani rai bai san abin da zai aikatãba a gõbe, kuma wani rai bai san a wace ƙasã zai mutuba. Lalle Allah Masani ne Mai bada labari 34}. [Suratu Luƙman: 34].
Na biyu:
Cewar Lallai ya rubuta wannan a Lauhul Mahfuz, dukkan wani abu da ya kasance, da kuma zai kasance to a rubuce yake a wurin Allah a cikin littafi.
Dalilinta:
Faɗin Allah - maɗaukakin sarki -: {Kuma a wurinSa mabũɗan gaibi suke, babu wanda yake sanin su fãce shi, kuma yanã sanin abin da ke a cikin sarari da kogi, kuma wani ganye ba ya fãɗuwa, fãce yã san shi, kuma bãbu wata ƙwãya a cikin duffan ƙasã, kuma babu ɗanye, kuma babu ƙẽƙasasshe, fãce yanã a cikin wani Littãfi mai bayyanãwa 59}. [Suratu Al-An'am: 59].
Na Uku:
Shine kowannce abu da yake faruwa da ganin damar Allah ne, babu wani abu dazai faru daga gare shi ko kuma daga halittarsa sai da ganin damarsa - maɗaukakn sarki -.
Dalilinta:
Faɗin Allah - maɗaukakin sarki -: {Ga wanda yaso daga cikinku to ya tsaya kan tafarki madaidaici 28 kuma ba komai kuke nufin aikatawa ba sai in Allah ya so, shine Ubangijin talikai}. [Suratu Al-Takwir: 28,29].
Na huɗu:
Imani da cewar dukkanin kasantattu ababen halittane Allah ya haliccesu, kuma ya halicci zatinansu da siffofnsu da motsinsu, da dukkanin wani abu acikinsu.
Dalilinta:
Faɗin Allah - maɗaukakin sarki -: {Allah ne ya halitta ku da abin da kuke aikatãwa 96}. [Suratu Al-Saffat: 96].

Amsa- Shine Zancan Allah - maɗaukakin sarki - wanda ba abin halitta bane.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Idan wani ɗaya daga mushirikai ya nemi tsarinka to, ka tsareshi har sai yaji zancen Allah}. [Surat Al-Taubah: 6].

Amsa- Itace dukkan wata magana ko aiki ko tabbatarwa ko siffar halitta ko kuma siffar halayya ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -.

Amsa- Dukkanin abinda mutane suka ƙirƙira acikin Addini, wanda bai kasance a zamanin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - da kuma sahabbansa ba.
Bazamu karɓi bidi'a ba, kuma zamu mayar da ita ne.
Saboda faɗin Annabi - tsira da amincin su tabbata agareshi -: "Dukkanin Bidi'a ɓata ce". Abu Daud ya ruwaito shi.
Misalin:
:Kari a Ibada, kamar ƙara wanki na huɗu a lwala, kamar taron Mauludi, wannan bai zo daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da sahabbansa ba.

Amsa- Jiɓintarwa: Shine son muminai da kuma taimaka musu.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Muminai maza da muminai mata sashinsu masoyan sashine}. [Surat Al-Taubah: 71].
Barranta:
Shine ƙin kafirai da kuma adawa dasu.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Haƙiƙa koyi kaykaykyawa gareku ya kasance ga Ibrahim da waɗanda suke tare da shi, a lokacin da suka cewa mutanensu lallai mu masu kuɓutane daga gareku da abinda kuke bautawa wanin Allah mun kafirce muku, adawa da gaba ta bayyana atsakaninmu da tsakaninku har abada har sai kunyi imani da Allah shi kaɗai}. [Suratu Al-Mumtahanah: 4].

Amsa- Allah ba zai karɓi wanin Addinin musulunci ba.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Duk wanda ya nemi wanin musulunci amatsayn Addini to ba za'a karɓa daga gareshi ba kuma a lahira yana daga masu asara 85}. [Surat Aal Imran: 85].

Amsa- Misalin magana: Zagin Allah - tsarki ya tabbatar masa -, ko Manzonsa - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -.
Misalin aiki:
Wulaƙantar da Al-ƙur'ani ko sujjada ga wanin Allah - maɗaukakin sarki -.
Misalin ƙudurin zuciya:
Shine ƙudurce cewa akwai wani da ya cancanci ibada wanda ba Allah - maɗaukakin sarki - ba, ko kuma cewa anan akwai wani mahalicci tare da Allah - maɗaukakin sarki -.

Amsa:
1- Babban Munafunci: Shine ɓoye kafirci da kuma bayyanar da imani.
Yana fitarwa daga musulunci, kuma shi yana daga kafirci mafi girma.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Lalle munafikai suna can ƙasan ƙasa na wuta, kuma ba zaka taɓa samar musu mataimaki ba}. [Surat Al-Nisa'i: 145].
2.Karamin munafunci:
Misalin: Karya, saɓa alkawari, da cin amana.
Wannan ba ya fitarwa daga musulunci, shi yana daga cikin zunubai, kuma maiyin shi abin bijirowane ga azaba.
Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata agareshi - yace: "Alamomin munafuki uku ne: Idan yai zance sai yayi ƙarya, idan yayi alƙawari sai ya saɓa, kuma idan aka amince masa sai yayi ha'inci". Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.

Amsa: Shine Annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Muhammadu bai kasance uban kõwa ba daga mazanku, sa dai Manzon Allah ne kuma cikamakin Annabãwa}. [Surat Al-Ahzab: 40]. Manzon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata agareshi - yace: "Nine cikamakin Annabawa babu wani Annabi baya na". Abu Daud da Tirmizi da Nasa'i da wasunsu ne suka ruwaito shi.

Amsa- Mu'ujiza itace: Dukkanin abinda Allah ya badashi ga Annabawansa na abubuwan da suka saɓa al'adu domin shiryarwa akan gaskiyar su, misali:
-Tsagewar wata ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -.
- Tsagewar kogi ga Annabi Musa - amincin Allah ya tabbata agareshi - da kuma nitsar da Fir'auna da rundunarsa.

Amsa- Sahabi: Shne dukkan wanda ya haɗu da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - yana mai imani dashi, kuma ya mutu akan musulunci.
- Muna son su, muna koyi dasu, kuma sune mafi alheri kuma mafifitan mutane bayan Annabawa.
Mafifitansu:
Sune halifofi huɗu:
Abubakar - Allah ya yarda dashi -.
Umar - Allah ya yarda dashi -.
Usman - Allah ya yarda dashi -.
Aliyu - Allah ya yarda dashi -.

Amsa: Sune matan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -.
Allah - Maɗaukakin sarki yace: {Annabi shine mafi cancanta ga muminai ga kansu, kuma matansa uwayansu ne}. [Surat Al-Ahzab: 6].

Amsa: Muna sonsu, muna jiɓintarsu, kuma muna ƙin duk wanda yake ƙinsu, bama wuce gona da iri akansu, sune matansa, da zuriyarsa, da 'Ya'yan Hashim da 'Ya'yan Muɗallab daga muminai.

Amsa: Wajibinmu: Shine girmamasu da ji da biyayya garesu a duk abinda ba saɓoba, da barin yi musu tawaye, da yi musu addu'a da yi musu nasiha a sirrance.

Amsa: Aljanna. Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Lalle ne Allah Yanã shigar da waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai a cikin gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu}. [Surat Muhammad: 12].

Amsa: Wuta, Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Ku ji tsoron wuta wacce makamashinta mutane da duwatsu an tanadeta ga kafirai 24}. [Surat Al-Baƙarah: 24].

Amsa:Tsoro, shine jin tsoron Allah da kuma uƙubarsa.
Kwadayi:
Shine kwaɗayin ladan Allah da gafararsa, da kuma rahamarsa.
Dalili:
Faɗin Allah - maɗaukakin sarki -: {Waɗancan, waɗanda suke kiran, sunã nẽman tsãni zuwa ga Ubangijinsu. Waɗanne ne suke mafĩfĩta a kusanci? Kuma sunã kwadayin sãmun rahamarsa, kuma sunã tsõron azãbarsa. Lalla ne azãbar Ubangijinka ta kasance abar tsõro ce 57}. [Surat Al-Isra'i: 57]. Kuma Allah - Maɗaukakin sarki - yace: {Ka bawa bayina labari, lalle nine Mai yawan gafarane, kuma Mai yawan jinƙaine 49. Kuma lallai azabata itace azaba mai raɗaɗi 50}. [Surat Al-Hujrat: 49-50].

Amsa- Allahu, Ubangiji, Mai yawan rahama, Mai yawan ji, Mai yawan gani, Mai yawan sani, Mai yawan azirtawa, Rayayye, Mai girma, zuwa wanin wannan na abinda ya shafi sunaye kyawawa da kuma siffofi maɗaukaka.

Amsa: ALLAHU, Ma'anarsa Allah abin bautawa da gaskiya, shi kaɗai yake bashi da abokin tarayya.
ARRABBU:
Wato Mahalicci Mamallaki Mai yawan azurtawa, Mai jujjuya al'amura, shi kaɗai yake tsarki ya tabbatar masa.
ASSAMI'U:
Wanda jinsa ya yalwaci kowanne abu, kuma yana jin dukkanin muryoyi akan saɓaninsu, da karkasuwarsu.
ALBASIRU:
Wanda yake ganin kowanne abu, kuma yana ganin komai ya ƙaranta ko ya girmama.
AL'ALIMU:
Shine wanda iliminsa ya kewaye kowanne abu, wanda ya wuce, dana yanzu, da kuma na nan gaba.
ARRAHMAN:
Wanda ramhamarsa ta yawalci dukkanin abin halitta da kuma rayayye, dukkanin bayi da sauran ababen halitta suna ƙarƙashin rahamarsa ne.
ARRAZZAKU:
Wanda agareshi ne arziƙin dukkanin halittu yake, daga mutane da Aljanu da sauran dukkanin dabbobi.
ALHAYYU:
Shine Rayayye wanda baya mutuwa, kuma dukkanin halitta zasu mutu.
AL'AZIMU:
Wanda yake da kamala da girma dukkaninsu, a sunayansa da siffofinsa da kuma ayyukansa.

Amsa- Musosu, kuma mu koma zuwa garesu acikin mas'aloli da abubuwan shari'a masu sauka, kada mu ambacesu sai da kyakkyawan abu, wanda ya ambacesu bada wannan ba, daga mummunan abu to wannan ba akan hanya yake ba.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Allah yana ɗaga darajojin waɗanda suka yi imani daga gareku, da waɗanda aka basu ilimi, Allah Mai bada labarine game da abinda kuke aikatawa 11}. [Surat Al-Mujadalah: 11].

Amsa- Sune muminai masu tsoron Allah.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Ku saurara, Lalle ne masõyan Allah bãbu tsõro a kansu, kuma bãzãsu kasance sunã yin baƙin ciki ba 62. Sune wadanda sukayi imani kuma sun kasance suna jin tsoron Allah 63}. [Surat Yunus: 62-63].

Amsa- Imani faɗa ne, da aikatawa da kuma ƙudurin zuciya.

Amsa- Imani yana ƙaruwa da biyayya, kuma yana raguwa da saɓo.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Abin sani kawai, mũminai sũne waɗanda suke idan an ambaci Allah, zukãtansu su firgita, kuma idan an karanta ãyõyinsa a kansu, su ƙãrã musu wani ĩmãnin, kuma ga Ubangijinsu suke dõgara 2}. [Surat Al-Anfal: 2].

Amsa- Shine ka bautawa Allah kamar kana ganinsa, idan baka kasance kana ganinsa ba, to shi yana ganinka.

Amsa- Da sharuɗɗa guda biyu:
1. Idan sun zama da tsarkakakkiyar niyya kuma saboda Allah -maɗaukakin sarki - ne.
2. Idan sun kasance akan karantarwar Annabi - tsira da amincin Alla su tabbata agareshi - ne.

Amsa- Shine dogara ga Allah - maɗaukakin sarki - akan dukkanin abinda zai janyo anfaninnika da tunkuɗe cututtuka, tare da riƙo da sabubba.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Wanda ya dogara ga Allah to shi ya isar masa}. [Surat Al-Dalaƙ: 3].
Ma'anar:
{HASBUHU}: Wato ya isar masa.

Amsa- Aikin alheri: Shine horo da dukkan biyayya ga Allah - maɗaukakin sarki -, abin ƙi kuma: Shine hani daga dukkanin saɓawa Allah - mai girma da ɗaukaka -.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Kun kasance mafificiyar al'umma da aka fitar da ita ga mutane, kuna horo da aikin alheri, kuma kuna hani daga abin ƙi, kuma kuna yin imani da Allah}. [Surat Aal-Imran: 110].

Amsa- Sune waɗanda suka kasance a kan irin abinda Annabi - tsira da amincin Alla su tabbata agareshi - da sahabbansa suka kasance akansa, acikin faɗa da aiki da ƙudirin zuciya.
An ambacesu da Ahlussunna ne:
Saboda binsu sunnar Annabi - tsira da amincin Alla su tabbata agareshi - da kuma barin ƙirƙira.
Waljama'a:
Domin cewasu sun haɗu akan gaskiya basu rarrabu acikintaba.